Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne cikin sakon Maulidi don tunawa da ranar haihuwar Ma'aiki (s) da ya aike wa al'ummar kasa inda ya ce musu kada su damu don kuwa gwamnatinsa tana iyakacin kokarinta wajen magance matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta a kasar musamman irin matakan da aka dauka cikin kasafin kudin shekara ta 2017 da zai gabatar wa 'yan majalisar kasar a jibi Laraba.
Shugaba Buhari ya taya allahirin al'ummar musulmi murnar ranar haihuwar Ma'aiki (s) din inda ya ce Nijeriyan ta amfana sosai daga koyarwar Ma'aiki (s) musamman bangarorin da suka shafi zaman tare cikin kwanciyar hankali, karimci, sadaukarwa, gaskiya da rikon amana wajen ciyar da kasar gaba.
A Nijeriyan a yau 12 ga watan Rabi'ul Awwal ne ake gudanar da bukukuwan Maulidi din don tunawa da ranar da bisa wasu riwayoyi aka haifi Manzon Allah (s).
Gwamnatin Tarayyar Nijeriyan dai ta ba da hutu a yau din a duk fadin kasar don ba wa musulmi daman gudanar da bukukuwan Maulidin.288